Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa ta fara wani cikakken horo kan yadda za a inganta ayyukan alkalan kotun daukaka kara ta hany.
Ministan Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arzikin kasa ta yanar Gizo, Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda Darakta-Janar na NITDA, Kashifu Inuwa ya wakilta, ya bayyana horon a matsayin wanda ya dace a irin wannan lokaci, yana mai cewa bangaren shari’a na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen ganin an zamanantar da aiyukan ta a fadin kasar nan
“Haɓakar barazanar da ba a yi wa gwamnati ba da suka mamaye duniya ya sa hukumar NITDA ta yi haɗin gwiwa da Kotun Daukaka Kara ta hanyar samar da cikakken bayanai ga alkalan ta dake nufin kare dimokraɗiyya da tsaron ƙasar.”
Pantami ya ce, “Yana da matukar muhimmanci ga bangaren shari’a a matsayin, wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan da su rungumi amfani da fasahar watsa labarai da fasahar sadarwa gaba daya domin inganta ayyukanta da habaka samar da kayayyakin aikin su”, in ji Pantami.