Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya a zabukan fitar da gwani na gwamnonin jam’iyyar PDP da na APC da aka sanya a ranakun Laraba da Alhamis a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Tunde Mobayo, ya ce babban sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP), Usman Alkali Baba, ya amince da tura karin ‘yan sanda, domin kara wa jami’an da ke aiki a Ekiti Gwarin Gwuiwa.
Mobayo, a cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan (PPRO), ASP Sunday Abutu, ya fitar, ya yi gargadin a kan duk wani nau’in magudin zabe da tashe-tashen hankula a duk tsawon lokacin zabukan jam’iyun biyu.
Ya kuma tuhumi ‘yan sandan da aka tura domin zaben da su kasance masu kwarewa tare da kaucewa duk wani nau’in cin hanci da rashawa yayin gudanar da ayyukansu.
CP ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da jam’iyyun siyasa da su wanzar da zaman lafiya da gudanar da rayuwarsu bisa ka’idojin zabe domin kaucewa Magudi.