A jiya Talata ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri na samar da aikin yi ga mutum dubu 774 a duk fadin kasarnan.
An dai zabi mutum dubu daya ne daga kowanne karamar hukuma 774 da ake da shi a a kasarnan, inda za a dauki masu sana’ar hannu aiki a rika biyansu naira 20,000 na tsawon wata uku.