Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya ta saki wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ne da jami’an sojojin Najeriya suka kama tun ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2020 a unguwar Imo River dake jihar Abia.
Wadanda abin ya shafa, Sunday Nwafor, mai shekaru 59; Uzonwanne Ejiofor, 48; da Wilfred Dike, mai shekaru 36, an tsare su a birgidiya 14 ta sojojin Najeriya Ohafia,dake jihar Abia sama da shekaru biyu, kamar yadda jaridar PUNCH ta tabbatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Kamfanin Jiragen Sama Na Azman Ya Dakatar Da Ayyukansa
A halin da ake ciki, Amnesty International a Najeriya, ta yi maraba da sakin mutanen uku.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Larabar da ta gabata, Amnesty International ta bukaci gwamnati da ta bayar da bayanai game da halin da sauran wadanda aka tilastawa bacewar da kuma tsare su ke ciki.
“Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya da su bayar da bayanai game da halin da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su aka tilasta bacewarsu da kuma tsare su ba tare da izini ba, su baiwa iyalansu da lauyoyinsu damar ganinsu, a gurfanar da su a kotu, ko kuma a sake su ba tare da wata hukuma ta shari’a da ake amfani da ita wajen tabbatar da ci gaba da tsare su ba,” sanarwar ta karanta a wani bangare.
Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, bai dauki waya ba ballantana amsa sakonnin WhatsApp dana kartakwana daga wakilinmu a daren Laraba.
A wani labarin kuma, Gwamna Fayemi Ya Bada Umarnin Gyara Hanyar Ekiti Cikin Gaggawa
Ana ci gaba da samun sulhu na dindindin na wani yanki na titin Ilawe-Ado-Ekiti da aka gaza yinsa, yayin da Gwamna Kayode Fayemi ya umarci injiniyoyi a ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar da su yi aiki tare da ‘yan kwangilar da ke kula da hanyar don gudanar da binciken nan take na hanyar da abin ya shafa.
Gwamna Fayemi ya ba da wannan umarni ne a lokacin da ya ziyarci sashin hanyar da ya lalace a Ilawe Ekiti da yammacin ranar Laraba, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta yi aiki don samar da mafita ta dindindin ga hanyar.