Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 27 ga wata, da Talata 28 ga Disamba, 2021; da kuma Litinin, 3 ga Janairu, 2022 a matsayin ranakun hutu na jama’a don bikin Kirsimeti, Ranar dambe da bukukuwan Sabuwar Shekara bi da bi.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya kiristoci da daukacin ‘yan Nijeriya mazauna gida da na kasashen waje murnar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ta bana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Laraba mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore. Mai taken, ‘Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 27, Talata 28th, 2021 da Litinin 3 ga watan Janairu, 2022 hutun jama’a.
An ambato ministan yana cewa, “Dole ne mu yi koyi da rayuwar Yesu a cikin ayyukansa da koyarwarsa a kan Tawali’u, Hidima, Tausayi, Haƙuri, Salama da Adalci, wanda haihuwarsa ke nuni.
“Wannan ita ce hanya mafi kyau don nuna Kristanci da kuma bikin haihuwarsa.”
Ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro abubuwa ne guda biyu masu muhimmanci ga bunkasar tattalin arziki da wadata, ya kuma bukaci kiristoci da ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin na bukukuwan wajen yin addu’o’in kawo karshen rashin tsaro da ke addabar al’ummarmu baki daya.
Aregbesola ya kuma umarci dukkan ‘yan Najeriya da su kiyaye duk wasu ka’idoji da aka gindaya na COVID-19 da ba na magunguna ba kamar sanya abun rufe fuska, yawaita wanke hannu da sabulu da ruwa, amfani da na’urar wanke hannu da kuma nisantar cakuduwa.
“Ku yi bukukuwan matsakaita ba tare da zakuduwa da yawa ba kuma ku kiyaye duk ka’idojin da hukumomin kiwon lafiya suka tsara. Dauke shi a matsayin wani alhaki na kashin kai don hana yaduwar cutar,” in ji Ministan.