• Gwamnatin tarayya ta ya ba da kokarin hukumomin tsaro na gida da na kasashen ketare kan kama Kanu da su ka yi.
• Ministan shari’a Abubakar Malami ne, ya yi wannan yabon a madadin gwamnatin tarayya.
• Ministan ya kuma ce hukumomin tsaron sun yi nasaran kama Kanu ne a ranar 27 ga wannan watar da muke ciki.
Gwamnatin tarayya ta ya bawa kokarin hukumomin tsaro na gida da na kasashen waje, na mara ma ta baya, da suka yi, na ganin an kama jagoran masu kokarin kafa kasar Briafra Mazi Nnamdi Kanu da kuma ganin an hukumta shi, kamar yadda doka ta tana da.
Ministan shari’a na Kasa Abubakar Malami ne, ya yi wanna yabon, a madadin gwamnatin tarayya a zantawar shi da kafafen yada labarai, a babban birnin tarayya Abuja.
Malami ya ce, a na zargin Kanu ne da laifin tunzura Al’uma, na yiwa kasa bore, ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da kafofin sadarwa na zamani, da su ka hadar da: gidajen rediyon, Talbijin, da dai sauran su.
Kazalika ya kuma ce, “Kanu ya tunzura wasu Al’uma musamman a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, wurin tayar da zaune tsaye, da ya yi sanadiyar asaran rayuka da dukiyoyin al’uma, da suka hadar da: Na fararan hula, jami’an Soji da na yan sanda, da na wasu hukumomin tsaron kasar nan, da dai sauran su” inji Ministan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Habasha ta ce zata iya kara kutsawa Makelle
Ministan shari’an ya kuma ce, “An Sami nasaran kama Kanu ne bisa irin jajirce wa, da hukumomin tsaro na gida dana kasashen ketare su ka nuna, na ganin an dawo dashi gida, kuma ya cigaba da fuskanta shari’ar da aka fara a baya, wacce ake tuhumarshi da laifuka 11 a gaban kutun” inji Malami.
A karshe Malami ya ce, hukumomin tsaro sun yi nasaran kama Kanu ne a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekarar da muke ciki.
Comments 1