Dr Adeleke Mamora, ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire (STI), ya ce gwamnatin tarayya za ta magance yanayin aikin ma’aikatan lafiya a Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar kungiyar likitocin Najeriya (NMA) karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Dr Uche Ojinmah suka kai masa ziyara a Abuja ranar Alhamis din nan.
Mamora ya ce gwamnati za ta yi kokarin inganta yanayin aiki da kuma biyan albashin ma’aikatan lafiya, musamman ma likitoci.
Ya ce tilas ne a daina fita da ma’aikatan lafiya, musamman likitoci zuwa kasashen ketare.
A cewarsa, gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don dakile halin da likitocin ke ciki da suke tafiya ketare.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mamora ya yi alkawarin kare muradun likitoci da ma’aikatan lafiya, la’akari da dabarunsu ga bil’adama.
KARANTA WANNAN https://dimokuradiyya.com.ng/samar-da-wadataccen-abinci-gwamnatin-tarayya-ta-gina-cibiyar-samar-da-injinan-noma-a-nasarawa/
Ya kuma bukaci kungiyar da ta ci gaba da rike amana da kuma gudanar da aiki daidai da rantsuwar kama aikinsu.
Tun da farko, Dokta Ojinmah, shugaban kungiyar NMA, ya bukaci ministan da ya tattauna wasu kalubalen kungiyar kamar yanayin aiki, kayan aiki da kuma albashi a taron majalisar zartaswa ta tarayya FEC a madadinsu.
(NAN)