Zainab Ahmed, Ministar kuɗi, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin yin ƙaramin kasafin kuɗi da za a yi amfani da shi wurin sayen riga-kafin cutar korona.
Ta bayyana cewa akwai yiwuwar aiki tare da ‘yan majalisa domin amincewa da ƙaramin kasafin kuɗin.
Ministar ta bayyana cewa nan da makonni biyu za a kammala shawara kan kuɗin da za a keɓe wurin sayen riga-kafin.
Ben Akabueze, Darakta a ofishin kasafin kuɗi, ya bayyana cewa ƙasar na dakon kyautar riga-kafi na kashi 20 cikin 100 na ƴan ƙasar.
A yanzu dai mutum 102,601 aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Najeriya, inda kuma mutum 1,373.