Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, a jiya ya ce za a sake bude filin jirgin saman na Malam Aminu Kano don jigilar kasashen duniya a ranar 5 ga Afrilun 2021.
Ya bayyana hakan ne a garin Abuja a yayin da yake bayani game da kwamitin da Shugaban kasa ya kafa kan COVID-19.
Ya kuma ce za a sake bude filayen saukar jiragen sama na Fatakwal da Enugu don zirga-zirgar kasashen duniya a ranar 15 ga Afrilu, 2021 da Mayu 3, 2021.
An rufe filayen jiragen saman ne, kamar nasauran mutane a duk duniya. Mun rufe filayen saukar jiragen mu saboda a nan ne kwayar Covid19 ta shigo kasar.
Mun sake bude wasu bayan la’akari da wasu abu, tare da sauran masu ruwa da tsaki. Babu wata muguwar manufa don sake buɗe Kano ko wasu filayen jirgin sama. Akwai matakai da za a bi, ”in ji Sirika.
Gwamnatin Tarayya, a farkon dokar hana zirga-zirga zuwa kasashen waje da na cikin gida, ta rufe filayen jiragen sama a Najeriya don hana shigowa da cutar.
Daga baya gwamnatin ta sake bude filayen saukar jiragen sama na Legas da Abuja domin zirga-zirgar kasashen duniya