Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace Gwamnatin Tarayya zata cigaba da haɗa hannu da ɓangaren Shari’a, domin ta tabbatar cewa ya samu gashin kai.
Buhari ya faɗi haka a lokacin bikin buɗe taron bikin jojin Najeriya na shekarar 2021 wanda ya gudana a Andrews Otutu Obaseki dake Cibiyar Horas da Ma’aikatan Shari’a ta Mohammed Bello a Abuja a ranar Litinin.
Shugaban wanda yaje Ƙasar Afirka ta Kudu ya samu wakilcin mataimakin sa Yemi Osinbajo SAN wanda yayi jawabin.
Babban Mai Taimakawa Mataimakin shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labaru Laolu Akande ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta naƙalto Shugaban Ƙasa na cewa “a jawabi na a wannan taro na shekarar 2019, na jaddada buƙatar tabbatar da samun matakan da zasu sanya a gudanar da shari’a cikin sauƙi a ƙasar.
“Abubuwan da muka koya a lokacin cutar Covid-19 sun bamu hanyoyin da za’a bi domin cimma waɗannan nasarori. Munga yadda ɓangaren Shari’a suka tashi domin tunkarar matsaloli.