By Abbas Yakubu Yaura
Shirin yin Afuwa na Shugaban Kasa (PAP) yace sama da tsaffin tsagerun Neja Delta 1,000 ne ake sa ran za a horar da su aiki tare da daukar ma’aikata a lokacin da kamfanin sarrafa rogo mallakin Jihar Bayelsa dake Ebedebiri a karamar hukumar Sagbama ya fara gudanar da cikakken aiki.
Shugaban rikon kwarya na shirin afuwa na shugaban kasa, kanal Millan Dixon Dikio mai ritaya, shine wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da yake duba kayan aikin a masana’antar, yace masana’antar sarrafa rogo tana samar da ton 60 a kowace rana wanda hakan zai taimaka wajen horarwa da kuma daukar aikin wakilan PAP, akan noman rogo da kuma sarrafa sitaci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Dikio wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na musamman kan ayyuka, Godwin Ekpo, yace ra’ayin ya yi daidai da tsarin PAP kan dabarun karfafawa na (TEM).
Sannan yace ana sa ran za a horar da tsoffin masu tada kayarar baya kan shirin na PAP kusan 1,000 wanda zasu daga darajar rogon kuma zasu yi aiki a matsayin masu noman rogo don ciyar da ayyukan masana’antar gaba.
Kazalika Dikio yace shawarar tura tsoffin masu tayar da kayar baya zuwa wurin ya kuma yi daidai da tsarin samar da abinci na shirin PAP.
Mashawarcin kan gudanar da ayyukan na cibiyar, Mista Adebowale Ayoade, ya bayyana ta a matsayin masana’antar sitaci mafi girma a Najeriya kuma na biyu mafi girma a yankin kudu da hamadar Sahara.