Gwamnatin jihar Yobe ta sake duba sa’o’in ya nayin zirga-zirgar ma’aikatan babur mai kafa uku a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro Dahiru Abdulsalam.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Za Su Binciki Kai Kawon Da Gwamna Abiodun Yano Yi a Ranar Zabe
Sanarwar ta ce, wannan bitar ta biyo baya ne don inganta tsaro a fadin jihar da kuma rage wahalhalun da matafiya ke fuskanta saboda kayyade lokacin da aka yi yanzu daga karfe 6:00 na dare na yin amfani da babur mai kafa uku na kasuwanci.
“Saboda haka, an umurce ni da in isar da cewa a halin yanzu ana duba lokutan aiki na masu tuka Keke Napep na kasuwanci daga 6:00 na safe zuwa 8:00 na yamma kowace rana daga ranar Juma’a, 3 ga watan Maris, 2023.
“Saboda wannan ci gaban, Gwamnan Jihar Yobe ya umarci dukkan hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da bin wannan umarni”, in ji Birgediya Janar Abdulsalam.
Har ila yau SA kan harkokin tsaro ya umurci shugabannin kungiyar masu baburan Keke Napep da motoci ta kasa (NACTOMORAS) reshen jihar Yobe da su yi taka-tsan-tsan tare da bayar da cikakken hadin kai wajen aiwatarwa da kuma bin wannan sabon umarnin.
Idan dai za a iya tunawa, a jihar Yobe, an umarci masu amfani da babur masu kafa uku su yi aiki daga karfe shida na safe zuwa karfe 6 na yamma a kullum.
Koyaya, tare da yin bita na sama, direbobi da fasinjoji yanzu za su more awanni 14 na ayyukan Keke Napep.
A wani labarin kuma, Tsohon Shugaban Kasa Jonathan, Da Wasu Za Su Karbi Lambar Yabo Ta African A Rwanda
Za a karrama tsohon shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan da wasu manyan ‘yan Afirka a karon farko na The African Heritage Concert and Awards wanda aka shirya gudanarwa a Kigali, Rwanda, ranar 1 ga watan Afrilu.
Har ila yau, tsohon shugaban kasar Tanzaniya, marigayi John Magufuli; Mataimakin shugaban kasar Laberiya, mai girma, Cif Dr. Jewel Howard-Taylor; Tsohon shugaban kasar Botswana, Lt.-Gen. Seretse Khama Ian Khama, da sauran fitattun ‘yan Afirka su ma za a karrama su.