Kasar Burundi za ta tura sojoji 100 zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a ranar Asabar mai cike da tashin hankali a matsayin wani bangare na rundunar yankin, kamar yadda wani babban jami’in sojan Burundi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Kungiyar kasashen gabashin Afirka bakwai ta tura dakaru a karshen shekarar da ta gabata a gabashin DRC, wacce ke fama da bullar mayakan sa-kai da suka hada da ‘yan tawayen Movement (M23) a ranar 23 ga watan Maris.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Yobe Ta Sake Duba Lokacin Zirga-Zirgar Masu Adai-Daita Sahu a Kananan Hukumomi 17
Yakin da ake gwabzawa a lardin Kivu ta Arewa ya raba mutane da dama da muhallansu tare da kara ta’azzara rikicin yankin, inda gwamnatin DRC ta zargi Rwanda da goyon bayan kungiyar M23 – ikirarin da Kigali ta musanta amma Amurka da wasu kasashen yammacin Turai ke marawa baya.
Mayakan sun sake fitowa bayan da aka samu kwanciyar hankali a karshen shekarar 2021, inda daga bisani suka mamaye yankuna a Arewacin Kivu, ciki har da yawancin yankin arewacin Goma babban birnin kasar.
Kungiyar EAC da ta gudanar da tarurruka da dama domin kwantar da tarzoma tare da yin kiran janyewar kungiyar M23 daga yankunan da ta mamaye, ta samar da rundunar yankin da nufin tabbatar da zaman lafiya a gabashin DRC.
Amma dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Goma a watan da ya gabata, inda suke zargin rundunar EAC da yin katsalandan wajen fuskantar kungiyoyin masu dauke da makamai.
A ranar Juma’a, wani babban jami’in sojan Burundi ya shaidawa manema labarai cewa “Kamfanin sojoji kusan 100 zai tashi gobe zuwa Goma”.
Za a jibge sojojin ne a Kitshanga da Kilorirwe – yankunan da ‘yan tawayen M23 suka mamaye a Arewacin Kivu – da kuma Sake, in ji shi bisa sharadin a sakaya sunansa.
Wata sanarwar manema labarai da EAC ta fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa za a jibge sojojin Burundi a ranar Asabar, sai dai ba ta yi karin haske kan adadin sojojin da za su je DRC ba.
Bisa wani sabon jadawalin da shugabannin gabashin Afirka suka dauka a watan jiya, “dukkan kungiyoyin da ke dauke da makamai, ciki har da kungiyar M23, dole ne su janye nan da ranar 30 ga watan Maris, biyo bayan wani tsari mai matakai uku da aka fara a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Ana sa ran dakarun yankin za su hada da sojoji daga kasashen Kenya da Burundi da Uganda da kuma Sudan ta Kudu. Amma ba a fayyace girman adadin da aka nufa ba.
Mayakan ‘yan tawaye sun addabi gabashin DRC tsawon shekaru da dama, yawancinsu gadon yakokin yanki ne da suka barke a shekarun 1990 da farkon 2000.
Kimanin mutane miliyan 5.5 ne suka rasa matsugunansu a cikin kasar ya zuwa watan Nuwamban bara, a cewar hukumar ta MDD.
Bugu da kari, fiye da miliyan daya ne suka tafi wata kasa makwabciyarta, inda sama da 500,000 suka nemi mafaka a Uganda kadai.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Za Su Binciki Kai Kawon Da Gwamna Abiodun Yano Yi a Ranar Zabe
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Frank Mba, a ranar Juma’a ya nuna cewa zai binciki zargin yunkurin Gwamna Dapo Abiodun zuwa wasu rumfunan zabe yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da aka yi ranar Asabar a jihar.
Daily Trust ta rawaito cewa, an samu bacin rai a ranar Asabar din da ta gabata lokacin da Abiodun ya zagaya wasu rumfunan zabe a Iperu-Remo, ciki har da inda abokin hamayyarsa kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu ya kada kuri’a.