Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da lasisin gudanar da dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar, Malam Wadatau Madawaki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau babban birnin jihar.
A cewarsa, matakin dakatar da lasisin makarantun masu zaman kansu ya zama dole domin a cikin makarantun masu zaman kansu 761 da aka gano a jihar, 450 ne kawai suke da lasisin da ko dai ya kare, ko kuma suna aiki fiye da karfin lasisin su, ko kuma cikin rashin yanayi mai kyau na koyar da Ilimi a Jahar.
Karanta nanMajalisa Zata Binciki Yadda Aka Kashe Biliyan 200 Domin Kidayar Al’ummar Nijeriya
Madawaki ya ci gaba da cewa, sama da makarantu 300 ne ke gudanar da ayyukansu ba tare da lasisi ba wafanfa basuda abin da ya kamata ace makaranta na dashi.
Madawaki ya kara da cewa gwamnati ta tsara dabarun yadda za a daidaita ayyukan makarantu masu zaman kansu domin samar da ingantaccen ilimi a fadin Jahar ta Zamfara.
Ya kara da cewa gwamnati ta yi isassun tsare-tsare domin gyara da farfado da fannin ilimi a jihar da nufin sake fasalin tsarin gaba daya domin a fitar da shi ta hanyoyi daban-daban.
Kwamishinan ya ce za a yi la’akari da yadda malamai a jihar za su samu horo da kuma sake horar da su baya ga karin girma da kuma biyan alawus-alawus da albashi domin kara musu kwarin gwiwa.
A wani labarin KumaINEC ta Shirya Tsaf Don Gudanar Da Zaben Imo – REC
Sannan kuma ya kammala maganarsa da cewar duk wanda ke da bukatar gudanar da makaranta mai zaman kanta a fadin jahar dole ya zo ma’aikatar Ilimi ta Jahar a tantance shi kuma a duba abubuwan da ya tanada a matsayin makaranta sannan a bashi lasisin gudanarwa.