Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 199 da shanu 97 ga makarantun karatun Al-Qur’ani a fadin jihar, kamar yadda kwamishinan harkokin addini na jihar, Dr Tukur Sani Jangebe ya bayyana.
Jangebe wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar Sani Nasarawa a wajen kaddamarwar ya bayyana cewa tallafin na nuna goyon baya ne daga gwamna Bello Matawalle zuwa makarantun karatun Al-Qur’ani domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NAFDAC Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Amfani Da Magungunan Tari Da Ake Yi A Kasar Indiya
“Muna kira ga Malamai da su sanya jihar Zamfara musamman da kasa baki daya a cikin addu’o’insu musamman a lokutan bukukuwa kamar yadda suke yi,” inji shi.
Ya taya al’ummar musulmi murnar wannan biki tare da yin kira ga al’umma da su rungumi zaman lafiya da nuna soyayya ga juna ba tare da la’akari da matsayin al’umma, addini ko kabilanci ba.
A wani labarin kuma, Buhari Zai Halarci Taron Naɗa Mahamat Derby a Matsayin Shugaban Chadi Na Riko
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lotinin din nan zai halarci bikin nada Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Chadi na tsawon shekaru biyu.
Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Lahadin nan a Abuja.