Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa ta gargadi masu shigo da kaya, masu rarrabawa, dillalai, da masu sayayya da su guji shigo da su tare da rarrabawa, siyarwa da kuma amfani da maganin tari mara inganci da aka yi a kasar Indiya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa,hukumar NAFDAC tana kula tsarawa da sarrafa masana’anta, shigo da su, fitarwa, rarrabawa, tallace-tallace, amfani da abinci, magunguna, kayan kwalliya, na’urorin likitanci, ruwa mai kunshe da sinadarai da kuma sinadaren kayan wanki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Zai Halarci Taron Naɗa Mahamat Derby a Matsayin Shugaban Chadi Na Riko
A ranar 5 ga watan Oktoba ne hukumar lafiya ta duniya ta fitar da wani gargadi a duniya game da maganin tari guda hudu na Indiya dake da alaka da mutuwar yara 66 a kasar Gambia.
Kayayyakin magungunnan guda huɗu sune Promethazine Oral Solution, Kofexmalin Baby Cough Syrup, Makoff Baby Cough Syrup da Magrip N Cold Syrup.
Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa “wanda aka bayyana cewa kamfanin ya kera wadannan kayayyakin shine Maiden Pharmaceuticals Limited (Haryana, India). Har ya zuwa yau, masana’antar kamfanin da aka bayyana ba ta ba da cikakken tabbaci ga WHO kan aminci da ingancin waɗannan samfuran magungunan ba.
Da yake zantawa da jaridar The PUNCH, mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na NAFDAC, Sayo Akintola, ya ce kayayyakin ba hukumar NAFDAC ta yi musu rajista ba, don haka bai kamata a rika yawo dasu ba.
“Muna sanar da jama’a cewa idan suka ci karo da irin su a kasuwa, ba hukumar NAFDAC ta amince da su ba, don haka mutane su guji hakan.
Da aka tambaye shi ko hukumar za ta kai samame a kasuwannin magunguna domin tabbatar da cewa kayayyakin ba sa yaduwa, Akintola ya ce, “Hukumar kula da harhada magunguna ta kan shiga kasuwa a matsayin jami’an bincike don tabbatar da cewa babu wani samfurin da hukumar NAFDAC ba ta amince da shi ba. Don haka ne muke gargadin cewa wasu adadin magungunan hukumar NAFDAC ba su amince da su ba, don haka ‘yan Najeriya su guje su.”
Har ila yau, sanarwar fadakarwa ga ma’aikatan kiwon lafiya da sauran jama’a da hukumar ta fitar kuma ta mika wa wakilinmu, ya bayyana cewa, duk wani rukunin kayayyakin da ake bukata a dauka ba shi da hadari.
A wani bangare an karanta, “Kayayyakin da ba su da inganci a cikin wannan faɗakarwar ba su da aminci wajen yin amfani da su, musamman ga yara, na iya haifar da mummunan rauni ko mutuwa a gare su.”
“NAFDAC tana kira ga masu shigo da kaya, masu rarrabawa, dillalai, da masu saye da sayarwa da su yi taka-tsan-tsan a cikin tsarin samar da kayayyaki don gujewa shigo da su, rarrabawa, sayarwa, da kuma amfani da maganin tari marar inganci. Duk samfuran likita dole ne a samo su daga masu ba da izini da wurare masu lasisi. Yakamata a duba sahihancin samfuran da yanayin jiki a hankali.”
A wani labarin kuma, Yakin Neman Zabe: Atiku Ya Isa Uyo, Yayin Da BoT Ya Kara Neman Wike
Jam’iyyar PDP a ranar Litinin din nan za ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a hukumance a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an kammala dukkan shirye-shirye kuma jiga-jigan jam’iyyar ciki har da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar sun isa babban birnin jihar domin yakin neman kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC da a halin yanzu ta je mulkin kasar.