Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce gwamnoni sun fi shugaban kasa alhakin ci gaban jihohinsu.
A jawabin da ya gabatar a wajen bikin Gabfest karo na 6, shirin shekara shekara na Ministan, Fashola ya kuma yi nuni da cewa gwamnonin jihohi ne ke da alhakin tsaron lafiyar ‘yan kasa a jihohinsu tare da gwamnatin tarayya.
Ya ce, “Ban san adadin mutanen da za su tuna da abin da ke cikin jawabina ba game da yadda na yi kokarin nuna yadda gwamnan jihar ta ke da muhimmanci ga ci gabana fiye da shugaban Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa tsaro aiki ne da kowa keda Alhaji wajen tabbatar da shi, ciki kuwa har da gwamnati.
“Wannan yana goyon bayan sashe na 14 2(b) na kundin tsarin mulki inda aka yi amfani da kalmar ‘tsaro’.
Ya tanadi cewa: ‘(b) tsaro da jin dadin jama’a su ne babbar manufar gwamnati,” in ji Fashola.
Ya kara da cewa, “Bai bayyana wace gwamnati da ra’ayina ba, ita ce kowace gwamnati; kananan hukumomi, jiha da tarayya.”
Ya ce, saboda haka tsaro ya kunshi fiye da tura jami’an tsaro.
Ministan ya ce, “Irin tura albarkatun zamantakewa da tattalin arziki ne don samar da yanayin jituwa,” in ji ministan.