Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC sun yi wata ganawar sirri a dakin taro na gwamnonin Kebbi da ke Abuja.
Gwamnonin sun tattauna ne kan babban taron jam’iyyar na kasa mai cike da cece-kuce tare da tabbatar da gudanar da babban taron jam’iyyar APC na watan Fabrairu.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ne ya bayyana haka a karshen taron sirrin da aka yi a daren Lahadi.
Ya ce kwamitin riko na jam’iyyar ne zai sanar da ranar da za a gudanar da babban taron.
Gwamna Bagudu ya kuma bayyana cewa gwamnonin sun kada kuri’ar amincewa da kwamitin riko na jam’iyyar, karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.