Jam’iyyar NNPP ta zargi gwamnonin Kudu maso Yamma da “lalata” sadaukarwar Marigayi, Obafemi Awolowo, a fannin ilimi.
Sakataren jam’iyyar na kasa, Dipo Olayokun ne ya bayyana haka a garin Abeokuta na jihar Ogun, yayin kaddamar da kungiyar goyon bayan Kudu maso Yamma ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwanso.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Najeriya Zata Kasance Cikin Aminci Karkashin Mulkin Tinubu – Aisha Buhari
Olayokun ya yi zargin cewa gwamnonin sun gaza a yankin da “manufofinsu marasa kyau” a fannin ilimi wanda a cewarsa ya lalata tsarin ilimi na yankin.
Shugaban jam’iyyar wanda ya bayyana ilimi a matsayin ginshikin ci gaban kowace al’umma, ya zargi gwamnonin yankin da lalata kokarin Awolowo a fannin ilimi.
Ya bayyana durkushewar ababen more rayuwa a makarantun gwamnati, rashin ingantattun malamai da kuma munanan tsare-tsare, da dai sauran wasu kalubalen da ke tunkarar fannin a yankin.
Ya ce, Kudu maso Yamma ta taba zama abin alfaharin kasar nan sakamakon ilimi kyauta da Awolowo ya samar, “amma abin takaici, gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma a yau, idan akwai wani yanki da suka kai sifili, to a bangaren ilimi ne.
“Su (gwamnonin Kudu-maso-Yamma) sun lalata mana ilimin da Awolowo ya shimfida mana a Kudu maso Yamma.
“Ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma kuma mutane irin mu sun ji dadin karatun Awolowo na kyauta tun muna kanana.
“Ilimi ya kasance tamkar wani abu a gare mu a Kudu maso Yamma domin Baba Awolowo ya ba da fifiko kan ilimi lokacin yana Firimiya. A lokacin da ya so zama shugaban Najeriya, yana da manyan ajandodi hudu, kuma na daya shi ne ilimi kyauta.
“Amma a yau a Kudu maso Yamma ilimi ya lalace ta fuskar abun ciki da inganci. A jihohin Kudu maso Yamma a ajujuwa muna da dalibai kusan 500”.
A nasa jawabin, ko-odinetan yakin neman zaben Kwankwanso na Kudu maso Yamma, Wasiu Ajirotuntun ya ce, Kwankwanso idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya zai mayar da kasar kan turbar daukaka.
Ya ce, “Ya zuwa yau, akwai sama da dalibai 432 a jami’o’i a kasashen waje da Najeriya da ke cin gajiyar ilimi kyauta, wanda Dakta Rabi’u Kwankwaso ya samar mu su.
“Shi (Kwankwanso) ya san darajar ilimi. Ba tare da ilimi ba. Don haka mu fito kan titi mu bayyana dalilin da ya sa za su zabi NNPP.”
Shugaban jam’iyyar a jihar Ogun, Sunday Oginni, ya yi alkawarin samar da jihar ga Kwankwanso a zabe mai zuwa.
A wani labarin kuma, Wata Mata Da Aka Gano Jami’ar DSS Ce Ta Yi Tsalle Ta Fada Kogin Lagoon
Wata Mata da ta yi tsalle ta fada kogin Lagoon a legas a ranar Alhamis da yamma an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, an gano ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Majiyar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wasu majiyoyi a ofishin sun bayyana cewa ita mai koyar da yaki ce da ba ta da makami wacce ta shiga alfarmar iyayenta da ke aikin kayan tufafi.
Kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta ruwaito, ‘yan watannin da suka gabata, Adedokun wacce ta cika shekara 30 da haihuwa, ta samu wasikar yabo daga babban daraktan hukumar ta DSS a matsayin wacce ta fi kowa yaki a tawagarta.