By Ishaq Dabai
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC, reshen Babban Birnin Tarayya FCT, tace hadurran hanya sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 137 a cikin watanni tara da suka gabata.
Kwamandan sashin na hukumar Mista Samuel Ochi, shine wanda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Juma’a a Abuja cewa hadurra 738 sun faru a Babban Birnin Tarayya Abuja daga watan Janairu zuwa Satumba, Yace jimillar mutane 3,616 ne hatsarin ya rutsa da su, ya kara da cewa mutane 1,334 suka jikkata daga hadurra.
“Motocin da abin ya shafa sun kai guda 10,062. Idan ka duba musabbabin wadannan hadarurruka, muna da babban abin dake haifar da afkuwar haruran keta haddi na sauri da kuma yin karo gaba da gaba 35 ne, ”in ji shi.
Kwamandan sashin ya kara da cewa hadurra sakamakon hatsarin tuki sun kai 75. Ochi yace yawancin hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri, amfani da tsoffin tayoyi da tafiye tafiyen cikin dare.
“A cikin watanni tara, 39 daga cikin wadannan mutane an yi rikodin su, yayin da motoci suka toshe hanyoyi bayan afkuwar hatsarin, wanda ke haifar da faduwa, takwas ne, sannan, muna da wasu kararraki guda bakwai.” Idan ka duba hanyar da wadannan hadarurruka suka faru, hanyar dake rikodin FCT da yawa ta yi hadari ita ce titin Abaji Dangote -Gwagalada
Ya shawarci masu ababen hawa da masu zirga zirga dasu guji tafiya cikin dare, saurin gudu da sauran ayyukan rashin hanya daka iya yin barazana ga rayuwarsu da ta sauran masu amfani da hanya.