Hukumar kula da manin’yata aikin hajji ta kasa reshen jihar Niger, ta tsawaita ranar Mai da wa maninyatar aikin hajjin shekarar 2020/2021 kudaden su da su fara ajewa.
Sakataren hukumar reshen jihar Alhaji Umar Makun Lapai ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake wa wasu daga cikin Maninyatan, da su kaje ofishin, domin neman maida musu da kudaden su.
Sakataran ya kuma tabbatar wa da Maninyatar da cewa, za’a Mai da musu da kudaden su kamar yadda ya dace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Mai Tawali’u ne, cewar Sakataren OPEC
Ya kuma shawar ci wadanda su ka ne mi a mai da musu kudaden su, da su ci gaba da hakuri, domin hukumar na bada takaddar amsan kudin ne rukunin bayan rukunin.
Makun ya ce, an tsawaita neman Mai da kudaden ne, zuwa ranar 27 ga watan Ogustan shekarar 2021. Kuma an yi hakan ne, domin bai wa wadanda ke bukatar a mai da musu kudaden su, damar cike fam.