Har yanzu babu tallafin man fetur – Gwamnatin Najeriya ga El-Rufai, ‘yan kasuwa
Gwamnatin Najeriya ta dage cewa an cire tallafin man fetur.
Gwamnatin tarayya ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da kungiyar masu sayar da man fetur ta Najeriya, kan ikirarin da suke yi na cewa tallafin na cigaba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu ta tsare mutane 5 bisa zarginsu da fashi da makami
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan a wata hira da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Nneamaka Okafor ya raba kwanan nan.
Ministan ya ce masu zargin cewa Gwamnati na bayar da tallafin kayan masarufi ya kamata su ba da shaida da gaskiya.
Ya jaddada cewa matsayar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan tallafin man fetur bai canja ba.
Sai dai ya bayyana cewa kowace Gwamnati tana da alhakin rage tasirin matsalolin tattalin arziki ga ‘yan Najeriya a kowane bangare, ba wai kawai a harkar Man Fetur ba.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Heineken Lokpobiri ya jaddada cewa tallafin man fetur abu ne mai matukar muhimmanci amma gwamnati ta bayyana matsayar ta.
“Ba na so in shiga cikin wannan batun. Al’amari ne mai matukar muhimmanci. Yakamata mu sami duk gaskiyar.
“A iya sanina, Shugaban kasa ya cire tallafin, kuma ya ci gaba da cire shi har yau.
“Duk wanda ya ce ana biyan tallafi, sai dai a bar mutum ya kawo gaskiyar lamarin, sannan mu yi magana a kai.
“Wataƙila sojojin kasuwa ba za su iya tantance shi ba, amma bari mu magance farashin kamar yadda yake a yau.
“Kowace gwamnati na da alhakin yin wasu abubuwa, ba kawai a bangaren man fetur ba, har ma a wasu sassa da dama, don rage tasiri da nauyi a kan ‘yan Najeriya,” in ji shi.
Ku tuna cewa El-Rufai ya ce gwamnatin Tinubu na biyan tallafin mai fiye da da.
Da take mayar da martani kan wannan ci gaban, kungiyar masu sayar da man fetur ta Najeriya mai zaman kanta ta goyi bayan tsohon gwamnan.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar IPMAN, Cif Ukadike Chinedu, ya ce farashin man fetur ya kamata ya kai kusan N900 ga kowace lita ba tare da tallafi ba.
“Na sha fada a baya cewa an dawo da tallafin PMS, kuma gwamnati ta ce karya ce,” in ji shi.
A wani labarin kuma:Kotun Ilorin ta tsare ƴan ƙungiyar asiri 14
A ranar Laraba ne wata kotun Majistare ta Ilorin ta bayar da umarnin tsare wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a kungiyar asiri ta Eiye.
Ana zargin su da hannu a rikicin kungiyar asiri da ya faru a karshen mako a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.