Wani dan Najeriya ta ja hankali jama’a a kafafen sada zumuntar zamani bayan ya ce har yanzu yana son matarsa duk da ta ha’ince shi har sau biyu, LIB ta ruwaito.
Mutumin mai amfani da suna @teekaykush a Twitter ya bayyana hakan ne yayin wani ma’aboci amfani da Twitter ya yi wata wallafa.
KU KARANTA: Ku shirya wa takarar kirista nan gaba – Matar Tinubu
Yace meyasa ake shawartar mata da su yi wa mazansu addu’a idan sun kama su suna lalata, yayin da ake ba maza shawarar su rabu da matansu idan sun yi lalata da mazan waje.
A bangaren mutumin ya ce sam ba haka bane inda yayi misali da kansa. Ya ce matarsa duk da ta ha’ince shi har sau biyu inda ta yi lalata da maza a waje, amma har yanzu yana son abarsa.
Kotu Ta Tura Matasa Biyu Gidan Maza Kan Yunƙurin Fitar Da Hotunan Tsiraici
Wadanda ake zargin Hillary Ogbodo mai shekaru 23 da Joseph Chukwudi mai shekaru 23 ana zargin su da daukar hotunan makwabciyarsu mace tsirara.