Hare-Hare Kan Jami’an ‘Yan Sanda Ya Isa Haka – IGP
A jiya ne babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana harin da ake kai wa jami’an ‘yan sanda a matsayin wanda ya sabawa doka da kuma cin mutuncin doka da oda.
Baba, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa, kuma cin mutunci ga kakin ƴan sanda, musamman yanda aikin su yake na gudanar da ayyukan hukuma da na doka a wurare daban-daban a fadin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin Tsaro Shi Zai Hana Zaɓen 2023 – IPAC
Ya yi gargadin cewa ba za a sake amincewa da kai hare-hare kan jami’an ‘yan sanda da mutanen da ke bakin aiki ba a karkashin ko wane irin salo ne “kamar yadda rundunar ke rike da rayukan ma’aikatanta.”
IGP ya umurci dukkan umarnin ‘yan sanda da tsare-tsare da su “tabbatar da cewa mutanen da ke kai farmaki kan jami’an ‘yan sanda, ba tare da la’akari da abubuwan da suka gabata an sanya su fuskanci fushin doka ta hanyar gaggawar gurfanar da su a kotunan da suka cancanta ba.
Sai dai ya gargadi jami’an da su guji tauye hakkin ‘yan kasa a yayin da suke gudanar da ayyukansu, yana mai cewa ‘yan Nijeriya su ma su mutunta ‘yancin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Ya ce hakan zai taimaka wa jami’an su ci gaba da aikinsu na yin hidima da kare lafiyar ‘yan kasa da kuma tabbatar da doka da oda.
A wani labarin kuma:Rashin Tsaro Shi Zai Hana Zaɓen 2023 – IPAC
Shugaban bada shawara na Jam’iyyu, Yabagi Yusuf Sani, ya koka da cewa rashin tsaro da ake fama da shi a sassan Najeriya na iya hana zaben 2023.