An kama wasu da ake zargin sune suka kai hari cocin Katolika ta St. Francis Catholic Church da ke Owo, a jihar Ondo.
Wani faifan bidiyo da ya karade kafafan sada zumunta na zamani ya nuna yadda jama’a ke zanga-zanga a cikin fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye.
Ana iya jin daya daga cikinsu yana cewa: “Suna so su kai su Akure ( wadanda ake zargin). Matasan sun fusata.”
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki cocin tare da kashe wasu masu ibada da suka hada da mata da kananan yara a Ondo.
Adadin wadanda suka mutu ya kai 40, yayin da wasu kuma suka samu raunuka a asibiti suna karbar kulawa.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa, wasu daga cikin maharan sun yi shigar burtu a matsayin gungun jama’a na masu ibada, kuma sun yi ta harbi da bindigu kirarAK-47.
Hukumar tsaron ta kuma sanar da cewa an gano wasu bama-bamai guda uku da ba su tashi ba a wurin.
Comments 1