Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da hare-haren ‘yan bindiga a karamar hukumar Mangu na jihar Filato, inda ya umurci hukumomin tsaro da su tabbata sun dakile sake aukuwar hakan domin kare rayuwar al’umma a yankin.
Shugaban kasar ya yi wannan Allah-wadai din ne a sanarwar da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis a Abuja. A cewar sanarwar shugaban kasa Buhari ya kira gwamnan jihar, Simon Lalong da rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a jihar da su binciko me ya faru da kuma abin da ya kamata a yi domin dakile sake aukuwar hakan.
Buhari ya nuna matukar kaduwarsa da damuwarsa bisa wannan lamari, inda ya nemi jami’an tsaro a jihar da su bunkasa yadda suke sanya ido domin bai wa al’umma kariya daga hare-hare.
Rahotanni sun bayyana cewa, Jami’an ‘yan sandan jihar Filato a ranar Alhamis ne suka bayyana cewa wadansu ‘yan bindiga sun kashe wadansu da ake kyautata zaton makiyaya goma sha biyu tare da jikkata mutum guda a kauyen Kulben dake yankin Kombun na karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
DSP Terna Tyopev, Kakakin ‘yan sandan jihar Filato, ya tabbatar da aukuwar hakan a garin Jos. A cewarsa lamarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis.