Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta sake kama Hassan Hassan, wani dan ta’addar Book Haram da ya tsere daga gidan yarin Kuje kwanan nan.
Idan a’a iya tunawa cewa, a ranar Talata ne ‘yan ta’adda suka kai hari cibiyar kula da Fursunoni ta Kuje tare da kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da ‘yan kungiyar Boko Haram da kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP).
Bayan haka, a ranar Juma’a gwamnatin tarayya ta bayyana 64 daga cikin fursunonin da ake nema ruwa a jallo da sunayensu da wasu bayanai da aka buga.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya fitar, ya ce an kama dan Boko Haram din da ya tsere da sanyin safiyar ranar Asabar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan harin da aka kai gidan kurkukun Kuje da kuma tserewar fursunonin a ranar 9 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 0130 na safe, wani Hassan Hassan ‘M’ wanda sunansa da hotonsa na daga cikin fursunonin da suka tsere daga shari’ar Boko Haram ko Ta’addanci. Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa a garin Keffi sun sake kama su.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Adesina Soyemi ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa wani wuri mafi aminci yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don neman sauran wadanda suka tsere tare da mika wadanda aka kama.
“Kwamishanan ‘yan sandan, ya yaba da kokarin ‘yan sandan na gudanar da aiki mai kyau, ya kuma tabbatar wa da jama’a irin kokarin da rundunar ke yi na tabbatar da zaman lafiya ga kowa da kowa.”