Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro da ‘yan banga da mafarauta sun ceto wata mace da aka yi garkuwa da ita.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa an ceto wata matar a ranar Talata ya kawo adadin wadanda aka ceto zuwa bakwai.
KU KARANTA KUMA Masu Garkuwa Da Fasinjojin Jirgin Kasan Edo Sun Nemi Kudin Fansa
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji 32 da ke tashar jirgin kasa ta Igueben da ke karamar hukumar Igueben ta jihar Edo suna jiran jirgin da za su hau.
Kakakin rundunar SP Chidi Nwanbuzor, ya ce an ceto mutane bakwai.
A Wani Labarin Kuma Akwai Fasfo Guda I40,000 Na Kasa Da Kasa Har Yanzu Ba A Karba Ba – NIS
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) a ranar Talata ta ce kusan fasfo na kasa da kasa guda 140,000 ne har yanzu ba a karba ba a fadin kasar nan.
Kakakin hukumar, Mataimakin Kwanturolan hukumar shige da fice (DCI) Mista Tony Akuneme, ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin dillancin labarai Na Kasa lokacin da ya kai ziyarar aiki ofishin fasfo na Alausa, a Ikejan jihar Legas.
Akuneme ya kuma ce kusan 40,000 daga cikin 140,000 na cikin ofishin fasfo na Alausa.