Wata mata mai suna Maryam Bobbo da mijinta da ‘ya’yanta hudu sun bace bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a daren ranar Litinin.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda ‘yan ta’adda a daren ranar Litinin suka kai harin bam a kan hanyar dogo daga Abuja zuwa Kaduna tare da kai farmaki kan wani jirgin kasa cike da fasinjoji.
A cewar wani mai amfani da shafin Twitter, @Muazzamz, ma’auratan da ‘ya’yansu suna cikin Fasinjojin jirgin kasan, inda haryanzu ba’a gansu ba tun bayan faruwar lamarin.
“Maryam Bobbo, mijinta da ‘ya’yanta har yanzu ba a gansu ba daga abin da ya faru a daren ranar Litinin, yayin harin jirgin kasa, Allah SWT ya dawo da su da rai da lafiya,” @Muazzamz ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata da yamma.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Gwamnatin Kaduna ta ce tana kokarin tantance dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin da jami’an tsaro da ke cikin jirgin yayin da wannan mummun lamari ya faru.
Comments 1