Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Tsohuwar Jaruma a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Kuma Furodusa Sapna Aliyu Maru tace ba zata manta da harkar fim ba domin ita ce ta zamo Silar duk wani abu da ta samu a rayuwar ta.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya in da take bayyana cewa.
“Magana ta gaskiya duk wanda ya sanni da harkar fim ya sanni, duk da cewar a yanzu na Dade ba na yin fim saboda harkokin da suke gaba na, Amma dai alhamdulillahi harkar fim ta yi mini komai.”
Mun tambaye ta ko nan gaba za ta dawo ta ci gaba da yin shirin fim?
Sai ta ce” In hali ya yi zan iya dawowa na ci gaba da yi, Amma dai a yanzu ko nawa fim din na kaina da na ke yi ba ni da lokacin da zan yi shi saboda harkar kasuwancin dana ke yi ba zata ba ni damar zama na yi shirin fim ba.
Kuma ka san ita rayuwa Kullum ana ci gaba ne don haka a yanzu na samu ci gaban da idan na ce zan yi fim kamar na koma baya ne saboda ka ga yadda harkar fim din ta zama a halin yanzu. “
Daga karshe jarumar ta yi Kira ga abokan sana’arta dasu rinka yin amfani da damar su a duk lokacin da suka sameta domin kuwa ita harkar fim wata harka ce da ko dai ka daina yi da ita, ko Kuma ita ta daina yi da kai.