Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a yau Lahadi ya bayyana cewa bai san wanda ya yi nasara ba a sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar.
Kalaman na Adamu na zuwa ne bayan dan takarar jam’iyyar, Gwamna Adegboyega Oyetola ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ademola Adeleke.
Oyetola ya samu kuri’u 375,027 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 13 na jihar inda ya zo na biyu bayan Adeleke a zaben.
Da aka tambaye shi don yin tsokaci bayan kammala zaben, gwamnan jihar ya ce shugabancin jam’iyyar APC a jihar za ta mayar da martani ga sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar bayan nazarinsa.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da sana’o’insu ba tare da tayar da rikici ko haifar da tashin hankali ba.
Sai dai rashin da ya yi a zaben na ranar Asabar, ya zo wa shugaban jam’iyyar APC na kasa da mamaki.
Adamu wanda ya bayyana a shirin talabijin na Arise a yau Lahadin , ya musanta cewa yana da masaniya kan wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Ya ce wa mai gabatar da shirin, “Da girmamawa ya dan uwana, da gaske nake jin haka daga gare ka. Ban ji sanarwar a hukumance daga INEC ba, wacce ita ce hukumar da ke da alhakin gudanar da zabe a Najeriya.
“Ban ji su ba tukuna. Da zarar na ji ta bakin INEC, zan iya samun damar amsa wannan tambaya ta musamman.”.
“Tsakanin ni da ku, ban ji ta bakin INEC a hukumance ba, kuma ban karanta takardun da kuke magana akai ba. Ina karanta wasu takardu a kan teburina kafin in yi karin kumallo na amma har yanzu ban yi hakan ba tukuna,” inji shi.
Da aka kara tambayarsa kan ko jam’iyyar za ta amince da shan kaye idan a karshe ya ga sakamakon zaben,?
Ya ce, “Ba na son riga-kafin halin da nake ciki. Akwai bukatar kuyi hakuri haƙuri. Tunda kun sami sakamakon, ku jira ni ma in na samu. Kuna iya komawa gare ni kuma zan yarda in yi magana game da shi.
“Har sai na ji ta bakin INEC a hukumance ko kuma jama’ata da ke binciken sun tabbatar da cewa sakamakon ne, ba shakka, zan bi shi. Amma jin sakamakon farko daga gare ku abu ne da ba za a yarda da shi ba. Kai ba INEC ba ne.”
A cewarsa, har yanzu bai yi magana da dan takarar APC ba bayan zaben da ya baiwa jam’iyyar adawa ta PDP nasara.
“Ban yi magana da shi ba tukuna,” in ji shi.