Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
Wani nazarin da Jaridar Dimokuradiyya ta gudanar a kan jarumai yan biyu Hassana Musa da Hussaina Musa, da su ka shafe tsawon lokaci a cikin harkar fim, mun gano cewar, duk da sun dade ana dama wa da su amma har yanzu, babu in da su ka je, shin matsalar su ce ko dai wani abu ne daban?
Duk da cewar suna da kyakyawar mu’amala a cikin masana’antar, don ba za ka ji wani abu ya hada su da kowa ba.
Wani abu dai da ya ke da muhimanci a cikin harkar shi ne Uban gida, to amma su wadannan yan biyun, gaskiya tun da su ka shigo ba su da tsayayyen Uban gida a cikin harkar, don haka wannan ma zai iya kawo musu matsala, domin kuwa harka ce ta wa ka sani, kuma wa ya sanka.
Tambayar da wakilin jaridar Dimukaradiyya ya yi musu ita ce, Ya ku ke samun kan ku a irin wannan rayuwar tsawon lokacin da ku ka shafe a cikin harkar fim?
KARANTA WANNAN LABARIN: Alhaji Ahmad Joda ya rasu
Sai Hussaina Musa ta ce “Gaskiya ne mun sha wuya a tsawon lokacin da muka shafe a cikin harkar fim, musamman a baya, amma da ya ke mun sa hakuri a ran mu hakan ba ya damun mu. Ko da an ba ka aiki za a saka ka a fim aka zo aka canza ba ma nuna damu wa.” Inji ta.
Ta ci gaba da cewa “Ita rayuwa in da za ka samu ka ci gaba, ai ba za ka rasa kalubale ba, musamman ma ga wasu daga cikin abokan sana’ar ka. Daga sun ga wani abu na alheri ya taho maka, wata maganar ma kawai za a fada ne don ka ji haushi, ka fasa yin wannan abin da a ke ganin nasara ne a gare ka. Don haka sai dai mutum ya ajiye kalubalen ya tunkari nasarorin. Amma dai a yanzu mun fara ganin nasara, don haka nan gaba kadan mu ma, za mu shiga sahun jaruman da a ke dama wa da su da yardar Allah” a cewar tagwayan.
Comments 1