A kokarin shi na ganin ya bunkasa rayuwar mata da karfafamu su gwaiwa a a fanni siyasa, da kuma ganin suna taka rawa a aiyukan Gwamnati, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da Ofishin matar shi, da aka yi shi a Sashin Ten Chalets dake gidan gwamnatin jihar a birnin Kano.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanar wa da babban Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Abba Anwar ya fitar a yau juma’a.
Kwamishiniyar kula da harkokin Mata ta jihar Dakta Zahara’u Umar Muhammad, Shugaban Ayyukan Binta Lawan Ahmad, da kuma Shugaban Mata na jam’iyar APC a Yankin Arewa maso Yamma Yahanasu Buba, sun ya ba wa kokarin gwamnan na samar da ofishin.
Lokacin da ya ke kaddamar da aikin Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, ” wannan ofishin an yi shi ne, domin matan jihar Kano baki daya, kuma na uwar gida Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje ce, wacce ta mike ba dare ba rana, domin ganin ta inganta rayuwar mata, a dukkannin kananan hukumomin jihar guda 44″ inji sanar war.
Kazalika Gwamna Ganduje ya yaba mata, kan kokarin da ta ke yi, na ganin an ta fi tare da mata a harkokin Gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hassana da Hussaina ko me ya Hana su tasiri a harkan fim?
“Ko wani lokaci ta na kokarin ganin an tafi tare da mata, shiyasa ma, mu ka samar da wannan ofishin, domin karfafamata gwuiwa wajan cika mata burin na ta, ta wannan bangaren, Kuma zamu ci gaba da tallafamata, domin ta inganta rayuwar wasu matan” inji shi.
Kungiyoyin mata da yawan gaske ne dai, su ka halarci wurin kaddamar da Ofishin, cike da farin ciki da an nasha wa, Wanda su ka hadar da na jam’iyun siyasa, da kuma wadanda ba na siyasa ba, domin yaba wa, da kuma ci gaba da jinjina wa Uwargidan gwamnan, bisa yadda ta ke tallafa musu.