By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa yayin da ake fargabar mutuwar mutane da dama bayan da wani jirgin ruwa ya kife a karamar hukumar Mai’aduwa ta jihar Katsina.
Buhari ya kuma yi gargadi game da amfani da kwale-kwalen da ba su dace ba, da cunkusa mutane fiye da kima da kuma rashin amfani da rigunan kare rai da ake dangantawa da tabarbarewar jiragen ruwa a kasar.
Jam’iyyar APC Ce Ta Jawo Rashin Hadin Kai A Najeriya – Atiku Ya Soki Gwamnatin Buhari
Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Abuja, shugaban ya ce lamarin ya yi matukar baci.
Jirgin ruwan yana dauke da galibin yara ne da suka dawo daga bukukuwan Sallah.
Buhari ya ce: “Tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘ya’yansu.
“A yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da aikin ceton da gwamnatin jihar da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, NIWA ke gudanarwa a wurin da lamarin ya faru, tare da fatan ceto fasinjojin da suka bata.
“An umurci NIWA da ta samar da ƙarin rigunan ceto ga al’ummomin yankunan. Ina addu’ar Allah ya jikan Wadanda lamarin ya shafa, ya kuma baiwa duk wanda ke cikin jirgin lafiya.”
Comments 1