Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 13 A Hanyar Neja
Mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Bida zuwa Mokwa a jihar Neja.
Daily Trust a ranar Lahadin da ta gabata ta tattaro cewa shida daga cikin wadanda suka mutu ‘yan mata ne da ke tare da sabuwar Amarya zuwa gidan aurenta a lokacin da lamarin ya faru.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: Super Eagles Ta Lallasa Kamaru Da Ci 2-0
An ce sun mutu a nan take. An kuma ce wani kanin angon yana cikin wadanda suka rasa rayukansu.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne a tsakanin kauyen Lukoro da kauyen Wuya da ke kan hanyar Bida zuwa Mokwa da yammacin ranar Juma’a.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Neja, Kumar Tsukwam wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin a jiya ya ce mutane 13 ne suka mutu.
Sai dai bai tabbatar da ko wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su na tare da sabuwar kawarsu da suka yi aure zuwa gidan aurenta a lokacin da lamarin ya faru kamar yadda aka sani.
“Har yanzu ban gano wannan bayanin ba, amma gaskiya ne, wani hatsari ya afku a Lukoro. Wata motar Toyota Corolla da wata motar bas ta Nissan sun yi karo da juna kuma abin bakin ciki, mutane 13 sun rasa rayukansu,” inji shi.