- Yanzu haka dai Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024
- ‘Yan wasan na Super Eagles suna da babban kalubale a gaban su inda za su kara da Angola a wasan kusa da na karshe
- Tuni dai ‘yan Najeriya suka barke da murna kan wannan Nasara ta Super Eagles
Yanzu haka dai Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 da suka fafata a yau Asabar
Ademola Lookman ne ya zura kwallaye biyu a kowane rabin lokaci inda Najeriya ta samu nasara a kan Indomitable Lions.
KARANTA WANNAN: Sabon Gwamnan Kogi Ya Nada Sakataren Gwamnati, Ya Rike Kwamishinonin Tsohon Gwamna
Yanzu dai ‘yan wasan Jose Peseiro za su kara da Angola a wasan kusa da na karshe na gasar.
Tun da farko Angola ta lallasa Namibia da ci 2-0 a wasan da suka fafata a zagaye na 16.
A wani labarin kuma, Jigawa: Gwamna Namadi Ya Kafa Kotunan Tafi Da Gidanka Domin Hukunta Masu Kunnen Kashi
Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya kafa kotunan tafi da gidanka guda biyar domin gurfanar da masu karya dokar tsaftar muhalli
Kafa kotunan tafi-da-gidanka an yi shi ne da nufin aiwatar da dokokin muhalli da tsaftar muhalli a jihar
Duk wanda aka kama da laifin karya dokar zai fuskanci fushin doka
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kafa kotunan tafi da gidanka guda biyar domin gurfanar da masu karya dokar tsaftar muhalli a duk wata.
Kwamishinan muhalli na jihar Dr. Nura Ibrahim Dandoka ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a lokacin tsaftar muhalli na wata-wata a Dutse babban birnin jihar.