Wani Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Pilato Mai Suna Honarobul Haruna Ibrahim Maitala ya riga mu gidan gaskiya.
Maitala wanda mafiya akasarin mutane suka fi sanin shi da Turakin Jere ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a hanyar Bade zuwa Gitata yayin da yake zuwa birnin Jos fadar gwamnatin jihar Pilato a jiya Juma’a.
Kamar yadda aka wallafa a Shafin Facebook, Maitala ya gamu da hatsarin ne da matukinsa da Mai bashi tsaro wadanda dukkanninsu sun riga mu gidan gaskiya.
Gabannin Rasuwar tashi shune dan majalisa mai Wakilatar Bassa da Jos ta Arewa a majalisar wakilan tarayya.