Hatsarin Tankar Mai Ya Hallaka Mutane 5 a Ogun
Akalla mutane biyar ne suka mutu a ranar Laraba, yayin da daya ya samu raunuka, a wani hatsarin mota da ya afku a gadar Iju, daura da Ota-Idiroko, karamar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun.
Hatsarin dai kamar yadda jaridar DAILY POST ta tattaro, ya rutsa da wata tankar mai dauke da dizal; Toyota Camry Mai lamba FKJ 132 HE; motar Golf ta Volkswagen; wani keken TVS mai lamba KSF 822 QL da babur.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗumbin Magoya Bayan APC Sun Shelanta Goyon bayan su ga PDP A Kwara
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce direban motar dakon mai mai lamba KTU 258 XT ya samu matsala a birki, inda ya faɗawa cikin motocin da abin ya shafa kafin su fada cikin rami.
A cewar Akinbiyi, mutane 11 – maza takwas da mata uku ne suka yi hatsarin.
“wasu mutane nagari ne suka ceto wanda aka jikkata zuwa asibiti kafin isowar mu, yayin da wadanda ake zaton sun mutu an kwashe su zuwa babban asibitin Ota.
Akinbiyi ya ce, “An kammala kwashe dukkan motocin da abin ya shafa sai dai tankar man dizal da ta fada cikin rami yayin da muke jiran jami’an NUPENG su yi jigilarsu kafin a kwashe gaba daya,” in ji Akinbiyi.
A wani labarin kuma: Ƴan Sanda Sun Damƙe Matasa kan buga Kuɗaɗen Bogi a Bauchi
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Ummar Maman Sanda ya kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu da kuma samar da kudaden jabu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, (PPRO), SP, Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana hakan a Bauchi ta wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.