HOTO: Yadda Buhari Ya Gudanar Da Sallah Ta Farko Bayan Ya Sauka Daga Mulki
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalansa sun bi sahun sauran musulmi domin yin bikin Sallah, a ranar Laraba.
Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau, ya raba hotunan tsohon shugaban kasa tare da matarsa da wasu ‘ya’yansa da kuma surukansa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Har yanzu Kwankwaso bai sanar da mu cewa zai koma APC ba – Galadima
Ba a san inda aka dauki hotunan ba yayin da Buhari wanda ya koma Daura, mahaifarsa a jihar Katsina, ya gana da shugaba Bola Tinubu a Landan kwanan nan.
Yayin da Tinubu ya dawo Najeriya bayan ganawar, babu tabbas ko magabacinsa ya yi haka.
Ga hotunan Buhari da ‘yan uwa:
A wani labarin kuma:Jam’iyyar PDP Ta Karbi Magoya Bayan Da Suka Sauya Sheka
Jam’iyyar PDP reshen jihar Taraba ta bayyana shirinta na karbar wadanda suka sauya sheka ciki har da wadanda suka dawo jam’iyyar.
Da yake bayyana hakan a ranar Alhamis a Jalingo, babban birnin jihar, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Abubakar Bawa, ya ce, “nan ba da jimawa ba, babbar jam’iyyarmu za ta fara karbar ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa masu rijista a nan Jihar Taraba.