Jihar Gombe ta tsawaita hutun Sallah zuwa ranar Juma’a
Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Yahaya, ya bayar da umarnin tsawaita hutun sallar Eid-el-Kabir zuwa ranar Juma’a.
A cewar wata sanarwar manema labarai da Jibrin Yusuf ya sanyawa hannu kuma aka saki a ranar Alhamis, a madadin mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar Gombe, Ahmed Abdullahi, ya bayyana hakan ne domin tabbatar da cewa ma’aikata sun ji dadin bukukuwan tare da takwarorinsu na kasa baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Jam’iyyar PDP Ta Karbi Magoya Bayan Da Suka Sauya Sheka
A wani bangare na sanarwar Yusuf ya ce, “An umurce ni da in sanar da ku cewa Mai Girma Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, (Dan Majen Gombe) ya amince da tsawaita hutun jama’a zuwa Juma’a 30 ga watan Yuni 2023 domin baiwa ma’aikatan jihar damar ci gaba da gudanar da Shagulgulansu. Bukin Eid-el-Kabir na bana tare da takwarorinsu na kasa baki daya.”
Yayin da yake musu fatan dawowar su cikin farin ciki a ranar Litinin, ya kara da cewa za a ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka.
“Mukaddashin shugaban ma’aikatan na yi wa daukacin ma’aikata da kuma daukacin al’umma barka da Sallah lafiya.
Yusuf ya kara da cewa “A halin da ake ciki, za a ci gaba da gudanar da dukkan muhimman ayyuka a duk lokacin hutun jama’a kuma ma’aikata za su koma bakin aiki a ranar Litinin 3 ga Yuli, 2023,” in ji Yusuf.
A wani labarin kuma:HOTO: Yadda Buhari Ya Gudanar Da Sallah Ta Farko Bayan Ya Sauka Daga Mulki
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalansa sun bi sahun sauran musulmi domin yin bikin Sallah, a ranar Laraba.
Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau, ya raba hotunan tsohon shugaban kasa tare da matarsa da wasu ‘ya’yansa da kuma surukansa.