Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya ziyarci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a gidan sa dake Yenagoa jihar Bayelsa a ranar Juma’a.
Obi ya gana da tsohon shugaban kasar a gidansa da ke Yenagoa a Bayelsa ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Gwamna Wike Ya Garkame Ofishin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar
‘Yan biyun sunyi ganawar sirri a yammacin ranar Juma’a a yayin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP gabanin zaben 2023.
Jonathan, wanda ya nuna damuwarsa cewa Najeriya ta rabu, ya bukaci Obi da ya hada kan Najeriya idan ya zama shugaban Najeriya a 2023.
Tsohon shugaban kasar ya yabawa Obi da ke neman zaben a wajen manyan jam’iyyun siyasa.
Obi ya samu rakiyar abokin takararsa Yusuf Baba-Ahmed da jiga-jigan jam’iyyar.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Adesina Bisa Rasuwar Mahaifiyarsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa Dr Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya Afirka AfDB, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Misis Eunice Adesina.
Shugaban, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya kuma jajanta wa ‘yan uwa da abokan arziki da kuma abokan magidantan, wanda tafiyarta ta samo asali ne na sadaukar da kai ga Allah, kaunar makwabta da kuma kyautatawa a cikin al’ummarta.