Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ba ta ƙaddamar da shirin ɗaukar aiki na sabbin ma’aikata ba.
A cewar wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar, Peter Afunanya, Ph.D, dole ce ta sa hukumar fitar da wannan sanarwa biyo bayan saƙonnin bogi da ƴan damfara ke aikawa mutane na cewar hukumar DSS ta fara shirin ɗaukar aiki.
“Ya zama wajibi jama’a su sani cewa babu wanda ake karbar kudinsa idan za a dauke shi aiki a hukumar DSS.”
Haka zalika, Afunanya ya ƙara da cewa, “ana daukar aiki a hukumar ne ta hanyar tantancewa, da kuma cancanta amma ba wai ta hanyar karbar kudaden mutane ba.”
KARANTA WANNAN: Allahu Akbar: Kanin Sarkin Daura da abokansa 2 sun yi hatsari, sun rasu
“Da wannan, hukumar ta yi gargadi ga al’umma da su sani cewa ana daukar mutanen da suka tsallake horo daban daban kuma wadannan suka cancanta ne kawai suke samun aikin.
“A wannan gaɓar, ya zama wajibi jama’a su yi hattara da ƴan damfara, domin gujewa fadawa a komarsu, tare da yin asarar kudade ko wata dukiyar. Da zaran mutane sun hadu da irin wadannan batagari, to su kai rahoto ga hukumar.
“Wadannan da kuma suke aikata wannan mummunar ɗabi’a ta damfarar mutane ta hanyar aika masu da sakonnin daukar aiki su ƙauracewa yin hakan tun kafin dubun su ta cika.
“Ya zuwa yanzu hukumar DSS na ƙoƙari wajen ganin ta dakile yawaitar masu damfarar mutane da sunan sama masu aikin yi a ma’aikatu na gwamnati na masu zaman kansu,” a cewar sanarwar.