A jiya Juma’a ce aka yi jana’izar gawar wani tsohon shugaban mulkin soja (MILAD) na jihar Imo, Kanar Tanko Kurah Zubairu Mai ritaya, a makabartar sojoji ta 1 Division of Nigerian Army dake jihar Kaduna.
Marigayin an nada shi Jagoran soji na jihar Imo a gwamnatin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha da Kuma Mai Wuka da Nama wajan samar da dawwamammen tsaro a yankin Gabashin kasar nan.
Da yake jawabi a wajen taron jana’izar da aka gudanar a cocin St Luke’s Military Church, Camilla Barracks, 44 Nigerian Army Referral Hospital, Kaduna, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana tsohuwar marigayin a matsayin mai gina jama’a kuma ginshiki ga bil’adama.
Gwamnan wanda kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Declan Emelumba ya wakilta, ya ce jihar ta yi bakin ciki da rasuwar.