Hukumar KWallon Kafa ta Duniya FIF ta sake tsawaita wa’adin dakatarwa da ta yi wa shugaban ta Sepp Blatter da wa’adin shekara shida.
Kazalika shi ma Sakataren Hukumar Jerome Valcke ya gamu da fushin hukumar irin na Blatter yayin dukkanin su aka ci tarar su Pam dubu dari bakwai da saba’in ko wannen su.
Wannan hukunci da zai dauke su har zuwa shekara ta 2028 an yanke musu ne bisa samun sa da hawan kawara wa dokokin hukumar.
Da ma dai a watan Octoban wannan shekara ne wa’adin Blatter mai shekara 85 zai cika, yayin da shi kuma Valcke mai shekara 60 nashi wa’adin zai kare a watan Octoban 2025.
Idan za a iya tunawa dai FIFA ta dakatar da Blatter ne na tsawon shekara takwas yayin da daga bisani ta rangwanta mishi zuwa shekara shida bisa samun shi da biyan cin hancin pam miliyan daya da digo uku ga tsohon shugaban hukumar wato Michel Platini.
Karar da Blatter ya shigar a shekara ta 2016 gaban Kotun Da’ar Wasanni bai yi nasara ba bayan da ta sanya kafa ta shure karar tashi.