Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, Mista Zubairu Mato, ya tabbatar da cewa mutane uku ne suka samu raunuka sakamakon wani jirgin kasa da ya awon gaba da wata mota da babur a Kano.
Mato ya shaidawa manema labarai a Kano cewa babu wanda ya mutu a hatsarin, inda ya kara da cewa direban motar ya tsallake rijiya da baya.
Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda ke cikin wata matafiyar babur, an kai su wani asibiti a birnin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a cikin babban birnin jihar.
“Babu mutuwa amma mutane uku, wadanda suka samu raunuka, jami’an mu sun kai su asibiti,” in ji Mato.
Wani shaidan gani da ido, Aminu Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da siminti ta nufo layin dogo a lokacin da jirgin ke gudu.
Abdullahi ya ce wasu mutane sun yi yunkurin tsayar da motar amma direban bai lura ba.
Ya ce, “Lokacin da direban motan ya yi kokarin ketare layin dogo, jirgin ya bugi motar da babur din a lokaci guda.”
Ya kuma ce an garzaya da wadanda abun ya shafa asibiti a sume. (NAN)