By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC reshen jihar Bauchi ta kama wasu mutane 113 wadanda suka karya ka’idar dokokin tuki a cikin mako guda daya gabata a jihar.
Kwamandan sashin na jihar, Yusuf Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Bauchi ranar Alhamis cewa 52 daga cikin wadanda suka aikata laifin sun gaza sanya na’urar takaita saurin gudu a motocinsu na kasuwanci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa yawan hadarurrukan da ake samu a jihar na da nasaba da kin sanya wadannan na’urorin.
“Tun daga farkon lokacin da aka fara aikin a ranar 17 ga watan Disamba, mun kama masu karya dokokin tuki guda 113 kuma kotun tafi da gidanka ta gurfanar da su musamman wadanda basu sanya na’urar ba.
“Manufar kafa kotun tafi da gidanka shine don rage gudu saboda yawan hadurran da muke samu a jihar ya yi yawa.
“Mun mayar da hankali kan shigar da na’urori masu takaita saurin gudu don dakile hadarurruka kuma shi yasa muke kama wadanda suka ki sanya na’urar,” in ji shi.
Abdullahi yace wadanda suka aikata laifin za su biya tarar da aka kayyade na kin sanya na’urar.
Ya bukaci direbobin ‘yan kasuwa a jihar dasu sanya na’urar saboda hukumar FRSC ba za ta amince da kin sakawar ba.
Sannan “Ya kamata su sanya na’urar dake rege gudu ta yadda za mu iya dakile hadarurruka a kan hanya,” in ji shi.
Comments 1