By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta yi watsi da kasafin kudin shekarar 2022 daga farkon Naira biliyan 109.8 da Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar zuwa Naira biliyan 114.3.
Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe-Abdullahi ya sanar da zartar da kasafin kudin ne bayan mataimakin shugaban masu rinjaye, Daniel Ogazi, ya gabatar da kudiri a kan haka kuma shugaban marasa rinjaye, Abel Bala, ya mara masa baya a zaman na ranar Laraba.
Ya bayyana cewa an kara kasafin kudin ne bayan da aka yi nazari a kan wasu sassan da aka ware saboda mahimmancin su da kuma ci gaban jihar baki daya.
Shugaban majalisar ya yabawa mambobin bisa jajircewarsu da kuma aiki tukuru wajen ganin an aiwatar da kasafin cikin gaggawa.
Sannan ya bada shawarar cewa a kori masu ba da shawara kan kudaden shiga da MDAs ke aiwatarwa wadanda ba su kara darajar kudaden shiga na cikin gida (IGR) na jihar ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Yace “Ya kamata a sami kyakkyawar fahimta tsakanin dukkan MDAs kan tsari da kuma kyakkyawar hanyar cimma manufofin gwamnati da shirye-shiryen gwamnati,” in ji shi.