By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalabe sama da miliyan 3.8 na barasa iri-iri na miliyoyin naira da aka kwace a watannin baya.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Harun Ibn Sina, ne ya bayyana haka jim kadan bayan lalata kwalaben barasa a Tudun Kalebawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
Ibn Sina ya bayyana cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano tana samun nasara a yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi, abubuwan maye, da dai sauran munanan dabi’u na al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar ta amince da lalata kayan maye, wanda hakan ya ba hukumar damar samun umarnin kotu daga babbar kotun majistare mai lamba 8 dake Gyadi Gyadi Kano, na lalata duk giyar da ke hannunta.
Kazalika “An haramta sayarwa, da kuma mallakar kayan maye a cikin jihar,” in ji Kwamandan.
Sannan ya yabawa gwamnatin jihar bisa jajircewarta na ganin ta magance matsalolin al’umma.
A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nanata kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da jin dadin ma’aikatan Hisbah.
Ganduje wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar karamar hukumar Albasu kuma shugaban kwamitin riko na majalisar dokoki kan harkokin addini, Alhaji Sunusi Batayya, ya bayyana jihar Kano a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya sakamakon jajircewar gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen yaki da ta’addanci. shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan al’umma.
Ya kuma bukaci jama’a da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar cusa kyawawan dabi’u ga ‘ya’yansu domin ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Kano ita ce jiha ta farko da ta kafa ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar nan wadda ta yi nisa wajen inganta zaman lafiya,” inji shi.