Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta lalata giya sama da kwalba 196,400 a cikin birnin Kano. Sanarwar ya fito ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun babban Sakataren Labaran Mataimakin Gwamna, Hassan Musa-Fage.
Da yake magana jim kadan bayan shiri fasa giyan a Kalemawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce addinin Musulunci ya haramta shan giya da duk wani abu da ka iya gusar da hankalin mutum.
Da ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, Ganduje ya bayar da tabbacin cewa dukkanin hukumomin shari’a a yankin za su samu Karin girma da goyon baya iri guda dana hukumar Hisbah domin basu dammar gudanar da ayyukansu.
Jawabin ya kawo inda gwamnan ke bayyana cewa jihar za ta ci gaba da marawa Hisbah sama da kowa musamman bayan kaddamar da Kwamandojin hukumar a kananan hukumomi 44 na jihar.
A nashi jawabin, Kwamanda Janar na hukumar, Sheikh Haroon Ibn Sina ya bayyana cewa hukumar ta yi nasara a wajen hana siyar da giya da shan sa a karkashin sashi na 401 na dokar jihar Kano.
Ya ce hukumar ta samu umurnin kotu na lalata sama da manyan motoci 12.