Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce Alhaji Ibrahim Abdullahi ya fara aiki a matsayin sabon Kwamishinan Zabe (REC), a Jihar Yobe.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun shugabar sashen wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar, Rifkatu Duku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kebbi Bagudu Ya Amince Da Nadin Sabbin Wasu Hakimai Biyu A Jihar
A cewar sanarwar, sabon REC din ya kasance “tsohon soja ne kuma ƙwararren shugaba” wanda ya yi aiki a yawancin hukumomin tarayya a ƙasar.
Sanarwar ta kara da cewa, har zuwa lokacin da aka sake nada shi sannan kuma aka tura shi jihar Yobe, Alhaji Abdullahi ya kasance tsohon kwamishinan zabe na INEC na jihar Bauchi.
Hukumar ta bayyana kwarin gwiwar da yake da ita a kan hidimar da ya ke yi wa kasarsa, ko kadan ba za ta kara amfani ba wajen tabbatar da sahihin zabe, mai imganci a jihar Yobe.
Sanarwar ta kara da cewa “Muna yi masa fatan samun nasara tare da yi masa addu’ar samun kyakkyawar dangantaka da duk masu ruwa da tsaki.”
A wani labarin kuma, Atiku yace har ya yi hasashen Mutuwar APC bayan Zaɓen 2023
Dan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi hasashen rugujewar jam’iyyar All Progressives Congress bayan zaben 2023.
Atiku ya fadi haka ne a yayin kaddamar da kungiyar yakin neman zaben PDP ta Matasa a Abuja, ranar Alhamis.
Dan takarar na PDP ya ce, “Gaskiya PDP ce kadai jam’iyyar siyasa, APC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kawance ne tsakanin CPC da jam’iyyar Tinubu, kuma mun ga yadda kawance ya bace a kasar nan cikin dare.